• Home  
  • Kotu ta ba belin mahaifi na – Bello El-Rufai
- Babban Labari

Kotu ta ba belin mahaifi na – Bello El-Rufai

Dan majalisar wakilai, Bello El-Rufai, dan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa Kotun Tarayya da ke jihar ta bayar da belin mahaifinsa. Daily Trust ta rawaito cewa a cewar dan majalisar, wanda ke cikin kotun lokacin zaman yayin da aka hana ‘yan jarida shiga, su na ƙoƙarin cika sharuddan belin da kotun […]

Dan majalisar wakilai, Bello El-Rufai, dan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa Kotun Tarayya da ke jihar ta bayar da belin mahaifinsa.
Daily Trust ta rawaito cewa a cewar dan majalisar, wanda ke cikin kotun lokacin zaman yayin da aka hana ‘yan jarida shiga, su na ƙoƙarin cika sharuddan belin da kotun ta gindaya.
Haka kuma, wani jigo a jam’iyyar ADC kuma na hannun daman El-Rufai, Hayatudeen Lawal Makarfi, ya tabbatar da batun, inda ya ce an daura wasu sharudda kan belin.
Ya kuma nuna kwarin gwiwar cewa za a cika sharuddan nan ba da jimawa ba.
Tun da fari Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta gurfanar da El-Rufai a kotun jihar Kaduna, inda aka dage sauraron bukatar belin zuwa ranar 21 ga watan Afrilu, 2026.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai