• Home  
  • Ƙasar Saudiyya Ta Tsawaita Zaman ‘Yan Sudan Da Suka Yi Umrah
- Labarai

Ƙasar Saudiyya Ta Tsawaita Zaman ‘Yan Sudan Da Suka Yi Umrah

Kasar ta kaddamar da wani shiri da zai bai ƴan asalin ƙasar da kuma waɗanda ke zama a can, damar karɓar bakuncin ƴan Sudan bayan sauya bizarsu ta Umrah zuwa ta ziyara.

Ƙasar Saudiyya Ta Tsawaita Zaman 'Yan Sudan Da Suka Yi Umrah a Bana

Saudiyya ta yanke shawarar tsawaita bizar ƴan Sudan da suka je domin yin Umrah.

Kasar ta kaddamar da wani shiri da zai bai ƴan asalin ƙasar da kuma waɗanda ke zama a can, damar karɓar bakuncin ƴan Sudan bayan sauya bizarsu ta Umrah zuwa ta ziyara.

Matakin na zuwa ne bayan umarnin da Yarima Bin Salman ya bayar na yin haka wanda ke cikin ayyukan jin kai da suka ɗauka na tallafawa mutanen Sudan, a cewar kamfanin dillancin labaran Saudiyya.

Hukumar kula da fasfo a ƙasar (Jawazat), ta fara shirye-shiryen tsawaita bizar ƴan Sudan ɗin da suka je yin Umrah waɗanda kuma suka kasa komawa gida saboda faɗa da ake ci gaba da yi a ƙasarsu

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000