Shugaban gasar La Liga ya bayyana cewa rabuwa da Busquets da Barcelona zai baita damar sake dakko tsohon dan wasanta Lionel Messi
Javia Tebas ya cewa sai Barcelona ta rabu da wani dan wasa mai jan kudi ne za ta iya sake dakko Messi da ta ke kwadayin dawo da shi kungiyar.
Busquets wanda shi ne Kyaftin din Barcelona a yanzu ya tabbatar da jita-jitar raba gari da kungiyar tasa ko da ya ke bai sanar da inda zai koma ba, amma ya nanata cewa sam baya son rabuwa da kungiyar ta Catalonia.
A bangare guda Messi wanda bayanai ke cewa PSG bata da Shirin sabunta kwantiraginsa, jita-jita na alakanta shi da komawa Saudiya da taka leda don bin sahun babban abokin dabinsa wato Cristiano Ronaldo da ya koma Al Nassr a watan Janairu, inda wata majiya mai kusanci da shi Leo ke cewa Saudiyan ta yi masa tayin da bazai iya kawar da kai ba