• Home  
  • Ƴan sanda sun tsaurara tsaro a cibiyoyin JAMB jihar a Jigawa
- Babban Labari

Ƴan sanda sun tsaurara tsaro a cibiyoyin JAMB jihar a Jigawa

Kwamishinan ƴan sandan Jihar Jigawa, CP Haruna A. Yahaya, ya kai ziyara cibiyoyin rubuta jarrabawar JAMB, don duba  yanayin tsaron wuraren da ake gudanar jarrabawar. Ziyarar tasa na da nufin tabbatar da cewa an gudanar da jarrabawar cikin kwanciyar hankali da lumana da kuma bin tsari, ba tare da an samu wata matsala ba. Kakakin […]

Kwamishinan ƴan sandan Jihar Jigawa, CP Haruna A. Yahaya, ya kai ziyara cibiyoyin rubuta jarrabawar JAMB, don duba  yanayin tsaron wuraren da ake gudanar jarrabawar.

Ziyarar tasa na da nufin tabbatar da cewa an gudanar da jarrabawar cikin kwanciyar hankali da lumana da kuma bin tsari, ba tare da an samu wata matsala ba.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Lawan Shiisu Adam, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar asabar.

Sanarwar ta ce kwamishinan  ƴan sandan ya yaba da yadda jami’an tsaron  ke gudanar da aikin bayar da tsaro, ya tabbatar da cewa duk wanda yayi yunkurin tayar da hankalin al’umma ba za a saurara masa ba.

A ƙarshe rundunar ƴan sandan ta tabbatar da cewa a shirye wajen ci gaba da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai