Shugaban hukumar wayar da kai ta ƙasa NOA, Mallam Lanre Issa-Onilu, ya buƙaci ICAN da su mayar hankali wajen ɗabbaƙa kyawawan ɗabi’un kishin ƙasa a matsayin muhimmin ɓangare na aikinsu a faɗin Najeriya.
Ya bayyana sana’ar akanta a matsayin ginshiƙi wajen inganta gaskiya, riƙon amana da kuma bayyana gaskiya a tsarin tattalin arziki.
Sanarwar ta fito ne ta bakin Mallam Bala Musa, Daraktan Sadarwa da Yaɗa Labarai na NOA.
An bayyana hakan ne a taron Makon Lissafi na Abuja 2026 mai taken jaddada dabi’u da ƙwarewa a matsayin tubalin ci gaban al’umma da tattalin arziki.
A nasa jawabin maraba, shugaban ICAN, Dakta Michael Nnachi Okpara, ya jaddada buƙatar samun ƙwararru a matsayin wata hanya ta inganta ɗabi’u
