Hukumar tsaron farin kaya ta Civil Defence  (NSCDC) reshen jihar Gombe, ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a ƙungiyoyin satar babura da na’urorin lantarki a sassa daban-daban na jihar. Kamen ya biyo bayan wasu samame da jami’an hukumar suka gudanar bisa bayanan sirri a ƙananan hukumomin Billiri da Balanga da Akko […]

Hukumar tsaron farin kaya ta Civil Defence  (NSCDC) reshen jihar Gombe, ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a ƙungiyoyin satar babura da na’urorin lantarki a sassa daban-daban na jihar.

Kamen ya biyo bayan wasu samame da jami’an hukumar suka gudanar bisa bayanan sirri a ƙananan hukumomin Billiri da Balanga da Akko da kuma Gombe, kamar yadda kakakin hukumar a jihar, CSP Buhari Sa’ad ya bayyana.

ɗaya daga cikin waɗanda aka kama shi ne Haruna Hamman mai shekara 19 daga ƙaramar hukumar Billiri, wanda ake zargi da satar wani babur ƙirar Boɗer mallakin Adamu Buba.

An ce, an sace babur ɗin ne a ranar 15 ga Afrilu, 2026, kafin jami’an sintiri na NSCDC suka gano tare da ƙwato shi a garin Gombe.

Haka kuma, Hukumar ta kama Nura Adamu mai shekara 29 daga garin Bambam da ke ƙaramar hukumar Balanga, bisa zargin karɓar wani babur ƙirar Jinchen Kasea da aka sace, wanda aka gano mallakin Victor Thomas na unguwar Tumfure a ƙaramar hukumar Akko.

A wani samamen daban kuma, jami’an hukumar sun kama Ishiyaka Ahmed mai shekara 20 daga yankin Arawa B da ke cikin birnin Gombe, kan zargin shiga gida tare da satar kwamfutoci, na’urorin intanet (router) da kuma na’urorin power bank.

NSCDC ta ce, bincike na ci gaba domin kamo sauran waɗanda ake zargi da tserewa daga ƙungiyoyin, yayin da za a gurfanar da uku daga cikin waɗanda aka kama a gaban kotu bayan kammala bincike.

Kwamandan hukumar a jihar, CC Jibrin Idris ya sake jaddada ƙudirin NSCDC na yaƙi da miyagun laifuka, tare da kira ga mazauna jihar da su riƙa bai wa hukumomin tsaro bayanan duk wani motsi da suke zargin bai dace ba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai