• Home  
  • APC za ta gudanar da zaɓen fitar da gwanin shugaban ƙasa a gobe Asabar
- Babban Labari

APC za ta gudanar da zaɓen fitar da gwanin shugaban ƙasa a gobe Asabar

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya za ta gudanar da zaɓen fitar da gwanin takarar shugaban ƙasa a gobe Asabar ta hanyar ƴartinƙe. Cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ta ce za a gudanar da zaɓukan a faɗin mazaɓun ƙasar 8,809. Shugaba Tinubu da Stanley Osifo ne ke neman tikitin tsayawa jam’iyyar takara a zaɓen […]

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya za ta gudanar da zaɓen fitar da gwanin takarar shugaban ƙasa a gobe Asabar ta hanyar ƴartinƙe.

Cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ta ce za a gudanar da zaɓukan a faɗin mazaɓun ƙasar 8,809.

Shugaba Tinubu da Stanley Osifo ne ke neman tikitin tsayawa jam’iyyar takara a zaɓen 2027.

Jam’iyyar ta ce duk wanda ke da katin rajistar jam’iyyar na da damar zaɓar wanda zai yi wa jam’iyyar takara.

Sanarwar ta ce za a tattara sakamakon zaɓukan kowace mazaɓa a ƙaramar hukuma, kafin akai shi babban cibiyar tattara sakamakon ta ƙasa da ke Abuja.

Jam’iyyar ta kuma naɗa tsohon shugaban majalisar dattawan ƙasar, Sanata Pius Anyim Pius a matsayin shugaban kwamitin zaɓen fitar da gwanin shugaban ƙasar.

Yayin da ta naɗa Sanata Ali Ndume a matsayin shugaban kwamitin ƙarɓar ƙorafe-ƙorafen zaɓen.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai