• Home  
  • Babu Sansanin Sojin Faransa a Maiduguri — Sojoji
- Babban Labari - Labarai

Babu Sansanin Sojin Faransa a Maiduguri — Sojoji

Rundunar Sojin Najeriya, ta musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewar an kafa sansanin sojojin Faransa a Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno. A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Kaftin Reuben Kovangiya, ya fitar. Kaftin Kovangiya, ya yi ƙarin haske cewa jami’in da aka gani a bidiyon ba sojan Faransa ba ne. Ya […]

Rundunar Sojin Najeriya, ta musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewar an kafa sansanin sojojin Faransa a Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Kaftin Reuben Kovangiya, ya fitar.

Kaftin Kovangiya, ya yi ƙarin haske cewa jami’in da aka gani a bidiyon ba sojan Faransa ba ne.

Ya ce mamba ne na ƙungiyar bayar da shawara kan harkokin soji ta Birtaniya (BMATT), wadda ke aiki tare da sojojin Najeriya wajen yaƙi da ‘yan ta’adda.

Ya yi gargaɗi kan yaɗa jita-jita da labaran ƙarya a shafukan sada zumunta.

Sojojin Najeriya sun jaddada cewa suna ci gaba da haɗa kai da abokan hulɗarsu na ƙasa da ƙasa domin magance matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai