• Home  
  • Hukumar RaYa Al’adu Ta Najeriya Za Ta Kaddamar Da Kirkirarriyar Fasahar Zamani
- Babban Labari - Labarai

Hukumar RaYa Al’adu Ta Najeriya Za Ta Kaddamar Da Kirkirarriyar Fasahar Zamani

Hukumar Rawa Ta Najeriya (National Troupe of Nigeria) a karkashin jagorancin Kaltume Bulama Gana, FSNA, na shirin  wani gagarumin taro domin kaddamar da kirkirarriyar fasahar zamani da zimmar karfafawa yara da matasa guiwa wurin kallo da sauraron wakoki, kade-kade da raye-rayen gargajiya. 

Hukumar Raya Al’adu Ta Najeriya (National Troupe of Nigeria) a karkashin jagorancin Kaltume Bulama Gana, FSNA, na shirin  wani gagarumin taro domin kaddamar da kirkirarriyar fasahar zamani da zimmar karfafawa yara da matasa guiwa wurin kallo da sauraron wakoki, kade-kade da raye-rayen gargajiya. 

Taron na National Troupe of Nigeria zai gudana ne a lambun hutun Queen Amina da ke Iganmu Jihar Legas ranar Asabar 21 ga Disamba 2024. 

Sabon shirin zai kawo cigaba da ba a taba ganin irinsa ba, wanda zai baiwa mutane daga kowane lungu da sako na duniya damar ganin kyawawan  al’adun Najeriya.

National Troupe of Nigeria na ganin cewa wannan yunkuri zai bai wa matasa damar sanin kyawawan al’adunsu na asali a matsayinsu na cikakkun ‘yan Najeriya. 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai