Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta ce ta kai wani samame mafi girma na yini guda a tarihin kafuwar ta kan wasu da ake zargin masu damfara ne ta kafar intanet, inda ta cafke wasu ‘yan kasashen waje 193 da wasu ‘yan Najeriya 599 a Legas.
Kakakin hukumar EFCC Wilson Uwujaren ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai jiya a Legas.
Uwujaren ya ce, daga cikin ‘yan kasashen waje 193 akwai ‘yan China da Larabawa da kuma ‘yan kasar Philippines, wadanda ya ce an kama su ne a lokacin da jami’an hukumar suka afka musu a wani sumame a Legas a ranar Talata 10 ga watan Disamba.
Ya ce, wadanda ake zargin sun hada da ‘yan China 114, ‘yan kasar Philippines 40, ‘yan Kazakhstan biyu, wani ɗan Pakistan daya da kuma dan Indonesia daya.
Ya bayyana cewa ana zargin wadanda aka kama da zama ‘ya’yan wata kungiyar masu zamba cikin aminci ta kafafen sada zumunta da damfara ta kafar intanet da sunan cryptocurrency.
“An kama wadanda ake zargin ne a wani samame na bazata a maboyarsu, suna zaune ne a wani katafaren ginin bene mai hawa bakwai wanda aka fi sani da Big Leaf Building.
“Binciken mu ne ya tabbatar da cewa ‘yan kasashen wajen suna zaune a gidan da ke lamba 7, Oyin Jolayemi Street, wanda mutane suke tunanin wani wuri ne da aka tana da domin horar da abokan cinikinsu na Najeriya.
“An gano da manyan kwamfutocin da katin SIM 500 na telcos na cikin gida wadanda aka siya don aikata laifuka.
- Muna Son Ganin Bayan Siyasar Banga A Kano – Dan Gowan
- An Yi Wa Manyan Hafsan Soji 656 Ritaya A Najeriya
Haka kuma kakakin hukumar EFCC Wilson Uwujaren ya ce an gano cewa “Manyan ‘yan damafarar a cikin harkar ‘yan kasashen waje ne, su suka dauki abokan aikinsu na Najeriya aiki don neman wadanda za su riƙa damfara ta kafar intanet. Kamar yadda jaridar daily trust ta bayyana