• Home  
  • An Sace Gwarzon Gasar Karatun Alƙur’ani A Katsina
- Babban Labari - Labarai

An Sace Gwarzon Gasar Karatun Alƙur’ani A Katsina

’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani, Abdulsalam Rabi’u Faskari, tare da mahaifinsa da ’yan uwansa a Jihar Katsina.

’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani, Abdulsalam Rabi’u Faskari, tare da mahaifinsa da ’yan uwansa a Jihar Katsina.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata a kusa da Labin Bangori, yayin da suke dawowa Faskari bayan Abdulsalam ya samu lambar yabo wadda Gwamna Dikko Radda ya ba shi saboda nasarar da ya samu a gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa karo na 39 da aka gudanar a Birnin Kebbi, a Jihar Kebbi.

Wani jami’in gwamnati a Faskari, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da sace su.

“Malam Rabe da ’ya’yansa biyar, ciki har da Abdulsalam, wanda aka sace su a Bangori a kan titin Yankara. Har yanzu ba mu ji komai daga gare su ba.”

Abdulsalam, wanda ɗalibi ne a sashen likitanci na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, ya samu matsayi na farko a gasar a ɓangaren maza bayan ya haddace Alƙur’ani.

Har yanzu ’yan sanda a Katsina ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000