Daniel Bwala mai Bai Wa Shugaba Bola Tinubu Shawara Kan Harkokin Yaɗa Labarai, ya ce akwai yiwuwar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya koma jam’iyyar APC mai mulki.
Daniel ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na TVC, inda ya ce babban aminin Obi, Valentine Ozigbo, ya koma jam’iyyar APC domin yin takarar gwamna.
“Kun san muna rage ƙarfin jam’iyyar LP kuwa?” in ji Bwala.
A baya, ya sha musanta jita-jitar cewa zai bar jam’iyyar Labour Party.
Kakakin jam’iyyar, Obiora Ifoh, ya yi watsi da wannan magana, inda ya bayyana cewar wasu ’yan siyasa ne ke ƙoƙarin lalata jam’iyyar.
“Abin mamaki ne ganin yadda wasu ke ƙoƙarin haddasa matsala tsakanin jam’iyyar da shugabanninta,” in ji Ifoh.