• Home  
  • Hisbah Ta Kama Ummin Mama, Kan Zargin Ta Da Yada Bidiyon Tsaraicin Ta A TikTok
- Babban Labari

Hisbah Ta Kama Ummin Mama, Kan Zargin Ta Da Yada Bidiyon Tsaraicin Ta A TikTok

  Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wata Matashiya mai suna Rukayya Ibrahim, wacce akafi sani da Ummin Mama, bisa zargin ta da yaɗa hotunan tsaraicin a dandalin TikTok. Mukaddashin babban kwamandan hukumar Hisbar na jihar Kano, Dakta Mujahedden Aminudden Abubakar, ne ya tabbatar da kama Matashiyar mazauniyar unguwar Medile a karamar hukumar Kumbotso […]

 

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wata Matashiya mai suna Rukayya Ibrahim, wacce akafi sani da Ummin Mama, bisa zargin ta da yaɗa hotunan tsaraicin a dandalin TikTok.

Mukaddashin babban kwamandan hukumar Hisbar na jihar Kano, Dakta Mujahedden Aminudden Abubakar, ne ya tabbatar da kama Matashiyar mazauniyar unguwar Medile a karamar hukumar Kumbotso Kano.

Dokta Mujahidin ya ce kama matashiyar Ummin Mama da suka yi, ya biyo bayan korafe-korafen da suka samu kan yadda ta ke yada tsiraici a shafin Tiktok, wanda hukumar ta ce yin hakan ya saba da shari’ar addinin musulinci da kuma al’ada.

Da ta ke bayyana nadamar ta Matashiyar Ummin Mama, ta tabbatar da cewar tan ɗauki bidiyon tsaraicin nata a baya, sai dai kuma ta ɗauki tsawon lokaci da dai na ɗorawa bisa karɓar shawarar saurayin ta.

Ummain Mama ta ci gaba da cewa, sai dai daga bisani wasu ƴan TikTok, suka rinƙa dawo da bidiyon suna ɗora su a shafukan su domin su samu mabiya, lamarin da yaja hankalin Hukumar Hisbar ya kai kan batun, amma dai ta yi nadama hakan ba za ta sake faruwa ba.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000