Ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, ya kwace filin sabuwar sakatariyar jam’iyyar PDP ta kasa dake birnin tarayya Abuja sakamakon rashin biyan haraji na shekaru 20.
Bayanin hakan na cikin wata wasikar da hukumar kula da ƙasa ta birnin tarayya Abuja ta aikewa jam’iyyar PDP, dauke da kwanan watan 13 ga watan Maris.
Daraktan sashin kula da ƙasa na Abuja Chijioke Nwankwoeze, ne ya sanya hannu akan wasikar a madadin minista Wike.
- Hisbah Ta Kama Ummin Mama, Kan Zargin Ta Da Yada Bidiyon Tsaraicin Ta A TikTok
- Gwamna Abba Kabir Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Gidaje Na Kano