• Home  
  • An Yi Jana’izar Dokta Idris Dutsen Tanshi
- Babban Labari - Labarai

An Yi Jana’izar Dokta Idris Dutsen Tanshi

Dubban Mutane daga sassan Najeriya ne suka Halarci Jana’izar Shaik Abdul’aziz Idris Dutsen Tanshi wanda Allah ya yi wa rasuwa a daren  Alhamis.

Daga Safiyanu Haruna Kutama

Dubban Mutane daga sassan Najeriya ne suka Halarci Jana’izar Shaik Abdul’aziz Idris Dutsen Tanshi wanda Allah ya yi wa rasuwa a daren  Juma’a.

An gudanar da Jana’izar ne a Masallacin idi na Game Village dake garin Bauchi.

Shaik Abdul’aziz Idris Dutsen Tanshi dai ya rasu yana da Shekaru 68.

ya bar ‘ya’ya 38 da jikoki da Dama Kuma matan sa 3.

Manyan Yan siyasa irin su tsohon matemakin shugaban Nigeriya Atiku Abubakar da kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a Wa’iqamatus Sunna JIBWIS da sauran manyan malamai tuni suka fara aikewa da sakon ta’aziyya tare da alhinin rasuwar sa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai