• Home  
  • Kotu Ta Sanya Alpha Chales A Hannun Beli Kan Zargin Bata Suna
- Babban Labari - Labarai

Kotu Ta Sanya Alpha Chales A Hannun Beli Kan Zargin Bata Suna

Kotun Majistret mai lamba 17 karkashin jagoranci mai Shari’a Huda Haruna Abdu, ta bayar da belin matashiyar yar Tiktok din nan Alpha Charles, wadda Ƴan Sanda suka gurfanar a gaban bisa zargin ta da laifin ɓata suna. Ƙunshin zargin ya bayyana cewar Alpha Charles, ta ɓata sunan Sadiya Haruna ta dandalin sada zumunta. Yayin da […]

Kotun Majistret mai lamba 17 karkashin jagoranci mai Shari’a Huda Haruna Abdu, ta bayar da belin matashiyar yar Tiktok din nan Alpha Charles, wadda Ƴan Sanda suka gurfanar a gaban bisa zargin ta da laifin ɓata suna.

Ƙunshin zargin ya bayyana cewar Alpha Charles, ta ɓata sunan Sadiya Haruna ta dandalin sada zumunta.

Yayin da aka karanta mata tuhumar ta musanta, kuma lauyoyin da suke kare ta sun roki beli, Inda kotun ta sanya ta a hannun beli a bisa sharadin mutum biyu da za su tsaya mata,

Kazalika, sharuɗan Belin sun bayyana cewa, dole ne masu tsayawar na ɗaya ya zama ɗan uwanta na jini, ɗayan kuma ma’aikacin gwamnati mai mataki na 16, idan ta tsere masu karbar belin zasu ajiyewa kotun Naira dubu ɗari biyar.

Sai dai lauyan Alpha ya bayyana wa kotun cewar, Sadiya Haruna ta ɗauki hoto da bidoyon Alpha a harabar kotun ta kuma yaɗa a dandalin Facebook, tare da wasu maganganu da suke zargi na batanci ne.

A don haka kotun ta nemi mai ƙara Sadiya Haruna, sai dai an neme ta sama ko ƙasa ba a ganta ba, an kuma umarci lauyanta da ya gabatar da ita.

A karshe  kotun ta sanya ranar 28 ga wannan watan Afrilun da ake ciki na shekarar 2025, don ci gaba da sauraron shari’ar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000