• Home  
  • Harajin Trump Ba Zai Sa Mu Mika Wuya Ba – China
- Babban Labari - Labarai

Harajin Trump Ba Zai Sa Mu Mika Wuya Ba – China

China ta dage cewa ba za ta mika wuya ba, duk da matsin da take fuskanta daga shugaba Trump na lafta mata haraji, amma ta ce idan an nemi ayi sulhu a shirye take. Ma’aikatar kasuwancin kasar ta ce kofar tattaunawa a buɗe take. Rahotanni sun ce dama sun jima cikin shiri, sannin cewa irin […]

China ta dage cewa ba za ta mika wuya ba, duk da matsin da take fuskanta daga shugaba Trump na lafta mata haraji, amma ta ce idan an nemi ayi sulhu a shirye take.

Ma’aikatar kasuwancin kasar ta ce kofar tattaunawa a buɗe take.

Rahotanni sun ce dama sun jima cikin shiri, sannin cewa irin wannan yanayi zai taso, kuma suna ganin Amurka ita tafi bukatar China.

Akwai rahotanni da ke cewa manyan masana tattalin arziki a jam’iyyar kasar ta kwaminisanci na tattauna hanyoyin taimakawa ‘yan kasar a wannan gaba da ake ciki na yakin kasuwanci.

Amurka ta lafta harajin kashi 125 kan kayayyakin China.

Yayin da ita kuma China ta mayar da martani da harajin kashi 84 kan kayayyakin Amurka.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai