Shugaban ƙaramar hukumar Hadejia Honarabul Ahmad Abba Ari, ya jagoranci ƙaddamar da buɗe shaguna 6 da hukumar samar da aikin ta Gwamnatin Najeriya (NDE) da haɗin gwiuwa da ƙaramar hukumar suka samar.
Hukumar ta NDE ta gina shagunan ne guda 4 yayinda ƙaramar hukumar Hadejia ta samar da guda biyu.
Da yake jawabi a wajen taron, Darakta janar na Hukumar samar da aikin ta ƙasa (NDE) Silas Ali Agara yace, gina irin waɗannan wurare na daga cikin manufofin gwamnatin tarayya na samarwa al’umma aiyukan yi, inda ya ce an zaɓi jihar Jigawa a matsayin ɗaya daga cikin jihohi 6 na shiyoyin Najeriya nan 6 da aka zaɓo jiha ɗaya daga kowacce shiyya don a aiwatar da wannan shiri.
- Arsenal Ta Yi Wasan Kura Da Madrid A Filin Wasa Na Emirates
- Gwamnatin Mulkin Sojin Nijar Ta Haramta Auren Jinsi
Silas Agara ya yabawa tsohon shugaban hukumar shige da fice na ƙasa (Immigration) Muhammad Babandede a bisa ƙoƙarin da ya yi na ganin an zaɓi ƙaramar hukumar Hadejia wajen gudanar da wannan shiri.
A nasa jawabin wakilin gwamnan jihar Jigawa, sakataren zartarwa na hukumar bunƙasa tattalin arziƙi da samar da aikin yi na jihar Dokta Habibu Muhammad Ubale, ya yabawa dukkan masu ruwa da tsaki na ganin wannan shiri ya kankama, yana mai bayyana shirin a matsayin daidai da ƙudirin gwamnatin jiha na samar da guraben aiyukan yi ga alummar Jigawa.
Tun da farko a jawabinsa shugaban ƙaramar hukumar Hadejia Honarabul. Ahmad Abba Ari yace gina shaguna biyu da ƙaramar hukumar ta yi, na daga cikin manufofinsa na aiki kafaɗa da kafaɗa da duk wani mutum ko al’umma dake burin cigaban yankin, ya yabawa hukumar ta NDE bisa wannan namijin ƙoƙari.
A nasa ɓangaren mai martaba Sarkin Hadejia Alh. Dokta Adamu Abubakar Maje Con, wanda hakimin Waje (Katukan Hadejia) Alh Iliyasu Ibrahim ya wakilta, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki wajen raba shagunan da su sanya ido kan waɗanda aka bawa shagunan don ganin sun yi amfani da su ta hanyar da ta dace.
Bikin bude shagunan ya samu halartar manyan jamian gwamnati, shugabannin ƙungiyoyin ƴan kasuwa, ‘yan siyasa da sauran al’ummar gari