Kungiyar Kiwon Lafiya na Duniya WHO ta bayyana cewa cututtukan dake kama zuciya na daga cikin cututtukan dake yi wa mutane kisan farat daya inda a shekara cutar na ajalin mutum miliyan 17.9 a duniya.
Kungiyar Kula da cututtukan dake kama zuciya ta Duniya ta bayyana cewa mutum daya cikin mutane hudu a Najeriya na cikin hadarin kamuwa da cututtukan dake kama zuciya.
Ciwon zuciya shi ne kan gaba wajen kawo ajalin mutane da dama a kasashe masu arziki, domin an yi kiyasin cewa a kowane rabin minti mutum guda na mutuwa a sanadiyar ciwon zuciya a kasashen Yamma, duk da ci gaban da suka samu wajen wayewa da fahimtar cututtukan zuciya da aikin tiyata na zuciya.

Likitoci a Najeriya sun koka da yadda cututtukan dake kama zuciya ke kisan mutane da dama a kasan.
A wani rahotan da aka saka a ‘Global Heart Journal’ ya nuna cewa akalla mutum kashi 30.9% na fama da hawan jini a Najeriya.
Rahotan ya nuna cewa yaduwar cutar ya banbanta da bangarorin kasan inda a Arewa maso Yamma na da mutum kashi 24.7% sannan Kudu maso Gabas na da kashi 33.3% dake fama da hawan jini a kasar nan.
Shugaban Kungiyar Zuciya ta Kasa Kingsley Akinroye ya bada matsaloli biyar da ya sa ake ci gaba da samun karuwa da yawan mutanen dake mutuwa yanzu cututtukan dake kama zuciya ke kisa a kasar nan.
- Rashin cin ingantacen abinci dake Inganta garkuwar jiki na daga cikin matsalar dake haddasa cututtukan dake kama zuciya.
Zamani ya shigo da sauye-sauye wanda haka ya shafi Ingancin abincin da ake ci a kasar nan.
yanzu mutane sun gwamnace cin abincin da ake girkashi cikin kankanin lokaci.
Jami’an Lafiya sun ce cin irin wadannan abinci na cutar da lafiyar mutum domin da dama daga cikinsu na da gishiri ko zaki ko Kitse wanda duk ke haddasa cututtukan dake kama zuciya.
Likitoci sun yi kira ga mutane da su yawaita cin kayan lanbu da ganyen da ake ci a abincin su domin guje wa kamuwa da matsaloli irin haka.
- Rashin motsa jiki na daga cikin matsalolin da ke kara haddasa yaduwar cututtukan dake kama zuciya.
Duk da cewa zamani ya kawo ci gaba amma ya kamo matsaloli dake cutar da lafiyar mutane inda a dalilin shigiwar motoci da sauran ababen hawa mutane basa takawa zu je inda za su sannan aiyukkan na yi wa mutane yawa da har basu da lokacin fita domin matsalolin jikinsu.
Likitoci sun ce yawan kiba na daga cikin matsalolin dake hana jini motsawa yadda ya kamata a jikin mutum inda a dalilin haka ake samun matsaloli da suka hada da hawan jini, ciwon siga da cututtukan dake kama zuciya.
Kungiyar Zuciya ta Kasa manya kashi 62.6% basa motsa jiki su inda daga cikin su akwai akalla mutum kashi 28.9% dake fama da kiba a jikinsu.
Rashin ware isassun kudade domin inganta fannin lafiya da rage tsadan farashin magungunan na Hana mutane yin gwaji akai-akai domin tabbatar da lafiyar su.
Jami’an asibiti sun yi kira ga gwamnati da ta ware isassun kudade domin inganta fannin lafiyar kasar nan domin ganin an samar da lafiya ta gari a farashi mai sauki wa mutane a Najeriya.
- ShanTaba Sigari da kwankwadar Giya Barasa
Shan giya barasa da zukan taba sigari na daga cikin abubuwan dake cutar da jijiyoyin dake daukan jini Suwaiba bangarorin jiki.
Likitoci sun ce cutar da wadannan jijiyoyi na daga cikin matsalolin dake hadassa cututtukan dake kama zuciya, shanyewar bangaren jiki da dai sauran su.
Sauran Matsalolin dake Hadassa Cututtukan dake kama Zuciyar. Jami’an asibiti sun ce damuwa shine babban matsalar dake kisan mutane da gwamnati ta kasa mai da hankali wajen ganin ta kawar da shi.

