• Home  
  • Kotu Ta Bada Umarnin Tsare Matashin Da Ake Zargi Da Furta Kalmar Damfara Kan A . A Zaura A Facebook
- Babban Labari - Labarai

Kotu Ta Bada Umarnin Tsare Matashin Da Ake Zargi Da Furta Kalmar Damfara Kan A . A Zaura A Facebook

Babbar kotun Tarayya mai lamba 3 da ke zamanta a Gyadi-gyadi, karkashin mai shari’a Simon Amobeda, ta aike da wani matashi mai suna Ahmad Ilyasu gidan ajiya da gyaran hali bisa zarginsa da laifin batawa Abdulsalam Abdulkareem AA Zaura, suna a kafar sada zumunta ta Facebook. Tunda fari dai kunshin zargin ya ayyana cewa matashin […]

Babbar kotun Tarayya mai lamba 3 da ke zamanta a Gyadi-gyadi, karkashin mai shari’a Simon Amobeda, ta aike da wani matashi mai suna Ahmad Ilyasu gidan ajiya da gyaran hali bisa zarginsa da laifin batawa Abdulsalam Abdulkareem AA Zaura, suna a kafar sada zumunta ta Facebook.

Tunda fari dai kunshin zargin ya ayyana cewa matashin ya yi amfani da shafin nasa na Facebook, inda ya kira A-A Zaura, da cewa Dan Damfara ne, zargin da matashin ya musanta.

Matashi Ahmad Ilyasu, ya ce bai san da batun zargin da ake yi masa ba, a nan ne lauyan da yake kare shi ya roki kotun da ta bada belinsa kasancewar zargin da ake yi wa matashin ya fada cikin zarge-zargen da za a iya bayar da Beli.

Sai dai bangaren masu kara sun yi suka akan rokon bada belin, inda suka ce suna tsoron ka da a bayar da belin matashin ya tserewa shari’a, ko kuma ya sake aikata makamancin laifin a don haka ne suka yi sukar.

Kotun ta sanya ranar 22 ga wannan wata na Yulin 2025, domin ta yi kwarya-kwaryar hukunci akan batun bayar da belin ko kuma akasin hakan

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000