• Home  
  • Ko Makiyan Buhari Sun San Bai Yi Sata Ba: Akpabio
- Babban Labari - Labarai

Ko Makiyan Buhari Sun San Bai Yi Sata Ba: Akpabio

Shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio, ya kwatanta marigayi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a matsayin shugaba na gari wanda ya mulki Najeriya ba tare da satar duƙiyar ƙasa ba. Akpabio, wanda ya bayyana haka a lokacin taron majalisar zartaswa da aka gudanar a Abuja don yi wa tsohon shugaban addu’o’i, ya ce masu sukarsa ma […]

Shugaba Tinubu Ne Ya Taimaka Wa Godswill Akpabio Wajen Zama Shugaban Majalisa ~ Ali Ndume

Shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio, ya kwatanta marigayi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a matsayin shugaba na gari wanda ya mulki Najeriya ba tare da satar duƙiyar ƙasa ba.

Akpabio, wanda ya bayyana haka a lokacin taron majalisar zartaswa da aka gudanar a Abuja don yi wa tsohon shugaban addu’o’i, ya ce masu sukarsa ma sun san cewa bai yi almubazzaranci da duƙiyar ƙasa ba lokacin da yake mulki.

“Maganar gaskiya ita ce Buhari mutum ne wanda ba a isa a tankwarashi ba. Bai guje wa nauyin da aka ɗora masa ba, mutumin da kuma ya bauta wa ƙasarsa yanda ake so.

“Shugaba ne da ya jajirce wajen yin mulki yanda ya kamata duk da kalubale da ya fuskanta. Hakan bai sa gwiwarsa ta sare ba, amma duk da haka wasu sun ki aminta da shi,” in ji Akpabio.

Taron majalisar zartaswar na musamman ya samu halartar shugabancin majalisar tarayya, ministoci, gwamnoni da kuma ƴaƴan marigayin.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai