Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da shirin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya ce dawo da tallafin zai kawo tasgaro ga sauye-sauyen da aka yi a ɓangaren man fetur.
Ya kuma ce hakan na iya rage sha’awar masu zuba jari a matatun mai na cikin gida, ciki har da matatar Dangote da sauran ƙananan matatun mai.
Onanuga, ya bayyana shirin Atiku ba zai ɗore ba.
Ya ce harkar man fetur a Najeriya ta samu sauyi sosai tun bayan da Shugaba Tinubu ya cire tallafin mai a watan Mayun 2023.
Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziƙi, Taiwo Oyedele, ya ce cire tallafin mai ya samar da Naira tiriliyan 15.8 ga Gwamnatin Tarayya da jihohi da Ƙananan Hukumomi tsakanin Yunin 2023 zuwa Disamban 2025.
A cewarsa, Gwamnatin Tarayya ta samu Naira tiriliyan 5.4, yayin da aka raba wa jihohi da Ƙananan Hukumomi Naira tiriliyan 10.4.
Tinubu ma ya soki shirin Atiku, inda ya ce hakan ya nuna rashin fahimtar yadda ake tafiyar da gwamnati da tattalin arziƙi.
Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, ya ce ’yan Najeriya ba su ga amfanin cire tallafin mai ba.
Ya ce shirin nasa zai tallafa wa matatun mai na cikin gida tare da taimakawa wajen rage tashin farashin fetur, ba tare da komawa tsarin biyan tallafin mai na baya ba.
Atiku, ya kuma ce kuɗaɗen da aka samu sakamakon cire tallafin ba su inganta rayuwar ’yan Najeriya yadda ya kamata ba, musamman a lokacin da farashin kayan abinci da sufuri ke ƙaruwa.
Sai dai masana tattalin arziƙi, Uche Uwaleke da Ken Ife, sun yi gargaɗi kan sake dawo da tallafin mai.
Sun ce tsohon tsarin ya biyan kuɗin ya ɗora wa gwamnati mai yawa kuma cike yake da cin hanci da badaƙala.
Uwaleke, ya ce bai kamata a auna nasarar cire tallafin da yawan kuɗin da gwamnati ta samu ba.
Ya ce ya kamata a duba ko an yi amfani da kuɗaɗen wajen inganta ayyukan gwamnati, samar da kayayyaki da inganta rayuwar ’yan Najeriya.
Sai dai wasu ’yan Najeriya sun ce cire tallafin ya ƙara tsananta musu rayuwarsu.
Wani ma’aikacin gwamnati, Ibrahim Abbas, ya ce abin da ma’aikata suka fi fuskanta tun bayan cire tallafin shi ne hauhawar farashin rayuwa da raguwar darajar kuɗin da suke samu.
Wani tsohon ma’aikacin gwamnati, Sule Aliu, ya kuma ce tsadar rayuwa ta fi yi wa ’yan fansho illa, tun bayan cire tallafin man fetur a shekarar 2023.
