• Home  
  • Sai ’yan Najeriya sun sayi litar man fetur N5,000 idan Tinubu ya zarce
- Babban Labari

Sai ’yan Najeriya sun sayi litar man fetur N5,000 idan Tinubu ya zarce

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP, Prince Adewole Adebayo, ya yi kashedin cewa sai ’yan Najeriya sun sayi man fetur kan N5,000 duk lita idan Shugaba Bola Tinubu ya zarce a Zaɓen 2027. Gargaɗin na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ɗan takarar, Kwamared Mark Adebayo, ya fitar a ranar Talata. […]

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP, Prince Adewole Adebayo, ya yi kashedin cewa sai ’yan Najeriya sun sayi man fetur kan N5,000 duk lita idan Shugaba Bola Tinubu ya zarce a Zaɓen 2027.

Gargaɗin na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ɗan takarar, Kwamared Mark Adebayo, ya fitar a ranar Talata.

A cikin sanarwar, Adebayo ya soki tsari da yadda manufofin tattalin arzikin gwamnatin mai ci yake tafiya, musamman cire tallafin mai da ƙyale Naira ta lalubowa kanta daraja, lamarin da ya ce na iya jefa tattalin arziƙin ƙasar cikin hauhawar farashi mai tsanani.

Ya danganta hasashensa da yiwuwar ƙarin faɗuwar darajar Naira, yana mai cewa ana shigo da man fetur a farashin dala, amma hakan yana durƙusar da darajar Naira kuma yana ƙara tsadar shigo da man.

Adebayo ya ce idan dala ta kai N3,500, kuɗin shigo da litar mai kaɗai na iya wuce N4,000, lamarin da ya soki cire tallafin mai gaba ɗaya, da cewa hakan zai hana gwamnati damar rage wa ’yan ƙasa raɗaɗin tashin farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.

Ya ce idan farashin ɗanyen mai ya tashi sakamakon rikice-rikicen ƙasashen duniya, ’yan Najeriya za su ji tasirin hakan kai tsaye a farashin man fetur, wanda zai iya ƙara hauhawar farashin sufuri da abinci.

A cewarsa, yawan kuɗin ruwa da bankin CBN ke karɓa na kuma ƙara wa ’yan kasuwar man fetur tsadar kuɗin shigo da mai, yayin da matsalolin tashoshin jiragen ruwa da rarraba man ke ƙara wasu kuɗaɗe a kan kowace lita.

Adebayo ya ce matsalolin tattalin arziƙin da ake fuskanta a yanzu sakamakon manufofin tattalin arzikin ƙasar da ya bayyana a matsayin “tsarin Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF” maimakon manufofin da suka fi mayar da hankali kan walwalar ’yan ƙasa.

Ya ce Najeriya ba za ta iya tafiyar da tattalin arziƙinta kan doron haraji, cire tallafin mai da rage darajar Naira ba tare da samar da kayayyaki a cikin gida ba.

Ya ƙara da cewa farashin N5,000 na man fetur ba almara ba ne, yana mai cewa hakan na iya faruwa idan aka ci gaba da tafiya da kan tsarin manufofin da gwamnatin Tinubu ke bi a yanzu.

Ɗan takarar ya yi alƙawarin cewa idan aka zaɓe shi a 2027, gwamnatinsa za ta farfaɗo da matatun mai na cikin gida ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati da ’yan kasuwa, tare da dawo da wasu matakan tallafa wa ’yan ƙasa domin rage musu raɗaɗin tsadar rayuwa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai