• Home  
  • Wani Ya Maka ‘Yan Kwamitin Unguwa A Kotu Saboda Sun Hana Shi Zuwa Hira Wurin Bazawararsa. 
- Babban Labari - Labarai

Wani Ya Maka ‘Yan Kwamitin Unguwa A Kotu Saboda Sun Hana Shi Zuwa Hira Wurin Bazawararsa. 

Wani mutum mai suna Yusif Musa ya shigar da ƙara a gaban kotun shari’ar Musulunci da ke Danbare, ƙarƙashin jagorancin Alkali Munzali Idris Gwadabe, yana zargin shugaban kwamitin unguwar Yankusa, Abdulaziz Isa, da hana shi zuwa zance wajen wata bazawara da suke soyayya da ita, mai suna Amira Abubakar.

A cewar rahoton Arewa Updates, a zaman kotun da aka yi ranar Talata, 2 ga Satumba, 2025, Yusif ya bayyana cewa soyayyarsa da Amira ta kai matakin da suka yi gwajin jini domin shirye-shiryen aure. Sai dai shugaban kwamitin unguwar ya hana shi ziyartar gidan bazawarar.

Yusif ya ƙara da cewa a duk lokacin da yake zuwa wajen Amira, yana kashe kuɗi wajen biyan kuɗin abin hawa, kuma sau da dama yana siya wa ɗanta kayan ciye-ciye kamar biskit da ssuransu, wanda kuɗin suka kai kusan naira dubu 70. Amma duk da hakan, shugaban kwamitin ya hana shi ganin bazawarsa.

Saboda haka, ya nemi kotu ta tilasta a biya shi kuɗaɗen da ya kashe a cikin soyayyar da aka katse.

Bayan sauraron ƙarar, Alkali Munzali Idris Gwadabe ya bayar da umarni a tura batun zuwa ofishin ‘yan sanda domin ci gaba da bincike kafin kotu ta ci gaba da sauraren shari’ar.

Sai dai kawo lokacin hada wannan labarin, bamu samu jin ta bakin ‘yan Kwamitin Unguwar YanKusa ba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000