Wata matar aure mai suna Hauwaʼu Abubakar, ’yar shekara 32, ta riga mu gidan gaskiya bayan da injin casar shinkafa ya ja rigarta a Tumu, cikin Ƙaramar Hukumar Akko ta Jihar Gombe.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 8 ga Satumba, 2025.
Ya ce, Hauwaʼu ta je wajen wani mai injin casar shinkafa, Muhammad Danjuma, mai shekara 29, domin sayen shinkafa. Sai dai yayin da injin ke aiki, tufafinta ya makale a bel ɗin injin, ya janyo wuyar ta har samu mummunan rauni a wuyanta.
- Elrufa’i Ya Bukaci Hukumar PSC Ta Binciki Yan Sandan Kaduna Kan Cin Zarafinsa
- An Buɗe Taron Sauyin Yanayi Na Afrika A Addis Ababa
Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Gombe, Bello Yahaya, ya yi ta’aziyya ga iyalan mamaciyar da mazauna yankin, yana mai bayyana wannan rashi a matsayin abin bakin ciki.
Rundunar ’yan sandan ta kuma gargadi jama’a musamman masu amfani da injina su kula da tsaron lafiyarsu ta hanyar:
- Gujewa kusantar inji yayin da yake aiki.
- Sanya kayan kariya a wuraren injiniya.

