• Home  
  • Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 5 A Masallaci A Zamfara
- Babban Labari - Labarai

Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 5 A Masallaci A Zamfara

Aƙalla mutum biyar ne suka rasu lokacin da ’yan bindiga suka kai hari wani Masallaci,  yayin da ake tsaka da sallar Asuba a garin Yandoto da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara. Shaidu sun ce maharan sun kutsa cikin Masallacin inda suka fara harbi ba tare da ƙaƙƙautawa ba, inda suka kashe mutum biyar […]

Aƙalla mutum biyar ne suka rasu lokacin da ’yan bindiga suka kai hari wani Masallaci,  yayin da ake tsaka da sallar Asuba a garin Yandoto da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.

Shaidu sun ce maharan sun kutsa cikin Masallacin inda suka fara harbi ba tare da ƙaƙƙautawa ba, inda suka kashe mutum biyar nan take tare da jikkata wasu da dama.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce maharan sun kuma yi awon gaba da wasu Masallata.

Ya bayyana lamarin a matsayin “rashin imani da ta’addanci.”

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin waɗanda suka ji rauni yanzu haka suna asibiti ana kula da su.

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya ce ba shi da labarin faruwar lamarin.

Harin na zuwa ne mako guda bayan makamancin irinsa a ƙauyen Gidan Turbe, wanda shi ma ke Ƙaramar Hukumar Tsafe, inda aka yi garkuwa da aƙalla Masallata 40 yayin da suke tsaka da sallar asuba.

A wani labarin kuwa, masu haƙar ma’adinai 100 ta ɓarauniyar hanya ake fargabar sun rasu bayan rami ya rufta musu a kauyen Kadauri da ke Ƙaramar Hukumar Maru, a jihar Zamfara.

Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya auku a ranar Alhamis, inda ramin ya rufe mutane da dama.

Kafin ceto waɗanda suka maƙale, rai ya yi halinsa, sakamakon ɗaukar lokaci da suka yi a ƙarƙashin ƙasa.

A halin yanzu, an tono gawarwakin mutum takwas; dukkaninsu mazauna ƙauyen Mekwanugga.

An kai garinsu domin yi musu jana’iza, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai