Kungiyar malaman jami’ar kimiya da fasaha ta Wudil, ASUU, dake jihar Kano, sun koka kan rashin iya tafiyar da shugabancin makarantar, da kuma sauran abubuwa muhimmai da ake gudanar da su, ba bisa doron doka ba.
Shugaban kungiyar malaman jami’ar ASUU dake garin Wudil, Dakta Aliyu Yusuf Ahmad, ne ya bayyana hakan bayan wani taro da kungiyar ta yi, a makon da ya gabata tare da cimma matsaya kan yadda ake tafiyar da jami’ar.
Malaman sun ce a baya sunja hankalin jami’ar kan abubuwan da suke faruwa, don daukar matakin gyara amma ba a gyara ba.
Kungiyar ta kara da cewa, akwai abubuwa da dama da jami’ar bata basu muhimmanci ba, wadanda suka danganci harkar koyo da koyarwa da kuma samar da Dakunan kwana na dalibai da gidajen zaman Malamai da Ajujuwan karatu da kuma ofisoshi duka jami’ar ta gaza samar da su tsawon shekaru masu yawa.
- Gwamnatin Kano Ta Bayar Da Umarnin Binciko Musabbin Mutuwar Kwamandan Yaki Da Kwacen Waya
- Tinubu Ya Nemi Sabbin Hafsoshin Soja Su Daƙile Sabbin Barazanar Tsaro
ASUUn ta zargi jami’ar da rashin bayar da muhimmanci kan karatun daliban, inda hakan yake sanya zangon karatun daliban yayi tsayi sosai har su wuce lokacin da aka shirya musu.
Haka zalika kungiyar ta ce ba a fitar da bayanan kashen kudin jami’ar yadda yakamata, inda kungiyar ta ce ta rubuta wa makarantar korafe-korafe da dama har yanzu ba a dauki mataki ba.
A karshe kungiyar ta yi kira ga gwamnatin Kano, ta shiga cikin lamarin don samun gyaran da daidaita harkar koyo da koyarwa yadda yakamata bisa doron doka.

