• Home  
  • Kotu Ta Dakatar Da Jam’iyyar PDP Gudanar Da Babban Taro Na Kasa
- Babban Labari - Labarai

Kotu Ta Dakatar Da Jam’iyyar PDP Gudanar Da Babban Taro Na Kasa

Babbar kotun tarayya ta umarci babbar jam’iyyar adawa a Najeriya Peoples Democratic Party (PDP) ta dakatar da shirin gudanar da babban taronta na ƙasa a wata mai zuwa. Rahoton jaridar Daily Trust ta ruwaito Mai Shari’a James Omotosho na bayar da umarnin bayan shigar da ƙorafi gabansa domin ya duba ko PDP ɗin za ta […]

Babbar kotun tarayya ta umarci babbar jam’iyyar adawa a Najeriya Peoples Democratic Party (PDP) ta dakatar da shirin gudanar da babban taronta na ƙasa a wata mai zuwa.

Rahoton jaridar Daily Trust ta ruwaito Mai Shari’a James Omotosho na bayar da umarnin bayan shigar da ƙorafi gabansa domin ya duba ko PDP ɗin za ta iya ci gaba da shirin gudanar da taro na 15 da 16 ga watan Nuwamba.

Ana ganin mutumu uku da suka shigar da ƙarar masu yi wa Ministan Abuja Nyesom Wike biyayya ne, wanda ya ci alwashin hana gudanar da taron sakamaon rigimar da yake yi da shugabancin jam’iyyar.

Masu shigar da ƙarar sun yi zargin cewa PDP ta gaza wajen bin dokokin mulkin jam’iyyar da kuma Dokar Zaɓe ta 2022 game da shirin gudanar da taron.

Lauyan masu ƙorafi ya faɗa wa kotun cewa PDP ba ta gudanar da zaɓukan shugabancin jam’iyyar ba a jihohi 14, inda ya nemi kotun ta duba ko hakan ya saɓa wa doka.

Kazalika, a kwanan nan Sakataren PDP na Ƙasa, wanda abokin siyasar Wike ne, ya shigar da ƙorafi ga jami’an tsaron Najeriya cewa shugabancin jam’iyyar sun saci sa-hannunsa a takardar da suka aika wa hukumar zaɓe Inec ta sanar da babban taron, zargin da PDP ta musanta.

Yayin babban taron da aka shirya gudanarwa, wakilai za su zaɓi sabon shugabancin jam’iyyar na ƙasa, wanda zai bai wa masu adawa da Wike damar sauke dukkan masu yi masa biyayya a cikin ƙunshin shugabancinta.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai