• Home  
  • Kotu Ta Sake Dakatar Da Babban Taron PDP
- Babban Labari - Labarai

Kotu Ta Sake Dakatar Da Babban Taron PDP

Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta sake dakatar da jam’iyyar PDP daga gudanar da babban taronta da take shirin yi a garin Ibadan na jiyar Oyo. Wannan shi ne karo na biyu da kotu ta hana gudanar da taron, wanda babbar jam’iyyar hamayyar ke shirin yi a ranakun 15 zuwa 16 ga watan Nuwamban […]

Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta sake dakatar da jam’iyyar PDP daga gudanar da babban taronta da take shirin yi a garin Ibadan na jiyar Oyo.

Wannan shi ne karo na biyu da kotu ta hana gudanar da taron, wanda babbar jam’iyyar hamayyar ke shirin yi a ranakun 15 zuwa 16 ga watan Nuwamban da ake ciki.

Haka kuma kotun ta hana INEC sa ido kan babban taron ko kuma amincewa da sakamakon taron wanda ake sa ran fitar da sababbin shugabannin jam’iyyar.

Sai dai kafin wannan hukuncin na biyu, wata kotun a jiyar Oyo ta umarci jam’iyyar da ta ci gaba da gudanar da shirye-shiryenta na babban taron, wanda hakan ya haifar taraddudi.

Mai shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, bayan tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya shigar da ƙara, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

Lamido ya shigar da ƙara ne yana buƙatar kotu ta dakatar da jam’iyyar daga zaɓen fitar da sababbin shugabanni, inda ya ƙalubalanci abin da ya kira hana shi shiga takarar da ya ce an yi.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000