Rundunar yan sandan jihar Kano, ta kama wani matashi mai suna, Abubakar Ibrahim dan shekaru 20, mazaunin unguwar Darmanawa, bisa zarginsa da bayyana kansa, a matsayin jami’in dan sanda da yaudarar mutane da kuma karbe musu kudi.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin sakon muryar da aikowa da MUHASA TVR, a ranar Litinin.
CSP Abdullahi Kiyawa, ya ce tunda farko sun karbi korafin ne daga wajen wani mai suna, Abubakar Umar, kan cewar wanda ake zargin ya bayyana masa cewa shi dan sanda ne, kuma yana da bidiyon da yake sanyawa yara kanana yan mata ido a cikin unguwar.
Wand ake zargi ya karbi kudi naira dubu dari da ashiri, a wajen mutumin bayan ya tsoratar dashi cewa zai fitar da faifayen bidoyin da yake dasu ga jama’a matukar bai bayar da kudin ba.
‘’ ya fada masa cewa idan bai bayar da wannan kudin ba, wannan bidiyon da yake ganin kananan yara yan mata shi yasa ya zo ya gaya masa don a kasha magana’’.
- Yan Boko Haram Da ISWAP 200 Sun Mutu Sakamakon Rikici A Tsakaninsu
- Yan Boko Haram Da ISWAP 200 Sun Mutu Sakamakon Rikici A Tsakaninsu
Bayan samun labarin ne kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin binciko wa tare da kamo shi a duk inda yake, inda a wasu lokutan yake bayyana cewa baturen yan sandan yankin ne ya aiko shi.
Tuni wanda ake zargin ya amsa laifin sa, tare da cewa shi ba dan sanda ba ne, kuma yayi hakan ne saboda yaga mutumin bashi da wayewa sosai shi yasa ya cuce shi.
Haka zalika rundunar taja hankalin jama’a , su kara kula da wanda suke zuwa su bayyana kansu a matsayin yan sanda don su cuce su ta hanyoyin dabam-daban su dinga kai korafin a ofishin yan sanda mafi kusa don daukar matakin da ya dace.
A karshe rundunar ta ce da zarar ta kammala gudanar da bincike zata gurfanar dashi a gaban kotu don ya fuskanci hukunci.
