• Home  
  • Abin da Bala Kaura ya ce kan rade-radin sauya shekarsa zuwa APC
- Babban Labari - Labarai

Abin da Bala Kaura ya ce kan rade-radin sauya shekarsa zuwa APC

Yayin da ake ci gaba da lissafa gwamnonin da suke sauya sheƙ zuwa jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad, ya ce yana nan a jamiyyarsa ta PDP daram. Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan jita-jitar da ake yaɗawa cewa yana shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC. Gwamnan ya musanta hakan […]

Yayin da ake ci gaba da lissafa gwamnonin da suke sauya sheƙ zuwa jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad, ya ce yana nan a jamiyyarsa ta PDP daram.

Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan jita-jitar da ake yaɗawa cewa yana shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Gwamnan ya musanta hakan ne a wata hira da BBC ta yi da shugaban jam’iyyarsa ta PDP a jihar Bauchi wanda ya yi magana da yawun gwamnan.

Pharmacist Sama’ila Adamu Burga, shugaban jam’iyyar PDP a jihar Bauchi, ya ce jita-jita ce kawai.

“Da wa aka yi? kuma da wa gwamnan na Bauchi ya yi shawarar sauya shekar? to duk wannan jita-jitace kawai da soki burutsu,” in ji shi.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai