Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da rage lokutan aiki ga ma’aikatan gwamnati a lokacin azumin watan Ramadan.
Gidan Rediyon Jihar Jigawa ya rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Shugaban Ma’aikatan Jihar, Muhammad K Dagaceri, ya sanyawa hannu a ranar Laraba 18 ga Fabrairu 2026.
Sanarwar ta ce bisa sabon tsarin, ma’aikata za su rika zuwa aiki daga karfe tara na safe zuwa karfe uku na rana a ranakun Litinin zuwa Alhamis, maimakon karfe biyar na yamma.
A ranar Juma’a kuma, za su rika zuwa aiki daga karfe tara na safe zuwa karfe ɗaya na rana.
Muhammad K Dagaceri ya ce an hakan ne domin saukaka wa ma’aikata Musulmi tare da ba su damar samun isasshen lokaci domin gudanar da ibadu da sauran ayyukan alheri a cikin watan mai alfarma.
A ƙarshe, sanarwar ta bukaci ma’aikata su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’o’i domin samun zaman lafiya da bunkasar tattalin arzikin jihar da kasa baki daya.

