Majalisar dokokin jihar Kano ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam, bisa wasu zarge-zarge da aka gabatar a kansa a gaban majalisar, ranar Alhamis.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawal Hussaini ne ya gabatar da ƙudurin tsige mataimakin gwamnan kan zarge-zarge da suka haɗa da almundahana da kuɗin gwamnati a lokacin da ya shugabanci wasu hukumomin gwamnati.
A kan haka ne majalisar ta ce, kamar yadda doka ta tanada, ta yanke shawarar sanar da mataimakin gwamnan game da matakin da ta fara ɗauka na tsige shi.
A watan Janairu ne gwamnan jihar Kano Abba Kabir ya sanar da sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki a matakin tarayya, daga jam’iyyar NNPP, wadda ya lashe zaɓe ƙarƙashin ta a shekarar 2023.
Sai dai mataimakin nasa Aminu Abdulsalam bai bi shi zuwa jam’iyyar ta APC ba.

