Tag: MAJALISSA

Siyasa

Majalisar Dattawan Najeriya na so a daina yi wa tubabbun Boko Haram afuwa

Majalisar Dattawan Najeriya ta buƙaci gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin gyaran hali da sake haɗa tubabbun mayaƙan Boko Haram cikin al’umma. Majalisar ta cimma wannan matsaya ne a zamanta na ranar Talata, sakamakon ci gaba da sace-sace da kashe jami’an soji da ƴanbindiga ke yi a ƙasar. Shugaban kwamitin majalisar kan rundunar sojin Najeriya, […]

Babban Labari

Majalisar dokokin Kano ta jingine tuhumar da take wa tsohon mataimakin gwamna Aminu Abdussalam

Majalisar dokokin jihar Kano tace ta janye tuhume tuhumen da take yiwa tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, biyo bayan ajiye mukamin sa na Mataimakin Gwamna Jahar Kano Majalisar ta bayyana hakan ne a zaman ta na yau karkashin Jagorancin Rt Hon Jibrin Isma’il Falgore. Da yake ƙarin haske dangane da lamarin, […]

Babban Labari Labarai

Majalisar dokokin Kano ta gabatar da ƙudurin tsige mataimakin gwamnan Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdulsalam, bisa wasu zarge-zarge da aka gabatar a kansa a gaban majalisar, ranar Alhamis. Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawal Hussaini ne ya gabatar da ƙudurin tsige mataimakin gwamnan kan zarge-zarge da suka haɗa da almundahana da kuɗin gwamnati a lokacin da ya […]

Babban Labari Labarai

Majalisar dokokin Najeriya ta ɗage zamanta

Majalisar dokokin Najeriya ta ɗage zamanta zuwa ranar 5 ga watan Maris mai kamawa. Tun da farko an tsara majalisar za ta koma zama ranar 24 ga watan Fabrairu. Sai dai cikin wata sanarwa da akawun majalisar, Kamoru Ogunlana ya fitar, ya ce majalisar ta ɗage komawar ne domin bai wa kwamitocinsa damar kammala ayyukan […]

Babban Labari Labarai

Majalisar Dokokin Ribas ta fara shirye-shiryen tsige Gwamna Fubara

Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta fara shirye-shiryen tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, lamarin da ya haddasa ruɗani a siyasar jihar. A zaman majalisar na ranar Alhamis, da Kakakin Majalisar, Martins Amaewhule, ya jagoranta, Shugaban Masu Rinjaye, Major Jack, ya karanta takardar zargin da ake yi wa gwamnan bisa aikata manyan laifuka. Ya […]

Babban Labari Labarai

Mako mai Majalisa za ta kada ƙuri’a kan ƙudurin ƙirƙirar sabbin jihohi

Majalisar Wakilai za ta ƙada kuri’a a ranakun 10 da 11 ga watan Disamba kan muhimman kudurorin gyaran kundin tsarin mulkin 1999, ciki har da kirkirar sabbin jihohi da kafa ’yan sandan jihohi. Mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Okezie Kalu, ya sanar da jadawalin a zaman majalisar, inda ya ce tattaunawa kan kudirin sauya kundin tsarin […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000