• Home  
  • Kotu ta ba EFCC izinin kama tsohuwar ministar jin ƙan Najeriya Sadiya Faruoq
- Babban Labari

Kotu ta ba EFCC izinin kama tsohuwar ministar jin ƙan Najeriya Sadiya Faruoq

Kotu a birnin tarayyar Najeriya Abuja, ta ba hukumar yaƙi da masu yi tattalin arzikin ƙasar ta’annuti EFCC, izinin kama tsohuwar ministar jin ƙai ta ƙasar Sadiya Umar Faruoq. EFCC na binciken tsohuwar ministar ne da badaƙalar dala miliyan $1.3m da kuma Naira miliyan N746.6m na ma’aikatar da ake zargin an wawure. A wani saƙo […]

Kotu a birnin tarayyar Najeriya Abuja, ta ba hukumar yaƙi da masu yi tattalin arzikin ƙasar ta’annuti EFCC, izinin kama tsohuwar ministar jin ƙai ta ƙasar Sadiya Umar Faruoq.

EFCC na binciken tsohuwar ministar ne da badaƙalar dala miliyan $1.3m da kuma Naira miliyan N746.6m na ma’aikatar da ake zargin an wawure.

A wani saƙo da EFCC ta wallafa a shafinta na X, ta ce mai shari’a Jude Onwuegbuzie, ya kuma ba da izinin kama sakataren ma’aikatar Bashir Nura Alkali.

Ta ce matakin ya biyo bayan ƙin bayyana a gaban kotu da waɗanda ake zargin suka yi a ranar Alhamis.

Lauyan waɗanda ake ƙarar sun buƙaci a ba su uzuri sakamakon rashin lafiya da hana Sadiya halartar kotun, amma kuma ba a amince da buƙatar tasu ba.

EFCC ta ce ta shigar da ƙarar ce tun a ranar 15 ga watan Disambar 2025, amma ba a samu damar yin ido biyu da waɗanda ake zargin domin miƙa musu takaradar kotun ba.

Sadiya ta riƙe muƙamin ministar ne a mulkin marigayi tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, inda daga baya ta auri tsohon babban hafsan sojin saman Najeriya AVM Sadiq Abubakar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai