• Home  
  • An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun
- Babban Labari

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Wani mai buga bulo ya riga mu gidan gaskiya bayan da wani da ake zargin ɗan daba ne, wanda aka fi sani da Aboy, ya daɓa masa wuƙa kan Naira 200 a wata gidan bulo da ke yankin Ota a Jihar Ogun. Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar 1 ga watan Afrilu a masana’antar […]

Wani mai buga bulo ya riga mu gidan gaskiya bayan da wani da ake zargin ɗan daba ne, wanda aka fi sani da Aboy, ya daɓa masa wuƙa kan Naira 200 a wata gidan bulo da ke yankin Ota a Jihar Ogun.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar 1 ga watan Afrilu a masana’antar bulo ta Ori-Ade, da ke kan titin Alaka, ƙarƙashin layin wutar lantarki a yankin Rosiji na unguwar Ewupe.
Majiyoyi daga cikin unguwar sun bayyana cewa wanda ake zargin ya tsere daga wurin da abun ya faru nan take bayan aikata laifin.

Daya daga cikin majiyoyin, wanda ya sakaya sunansa da Moyo, ya ce rikicin bai ɗauki lokaci mai tsawo ba kafin ya rikiɗe ya zama ajalin mutum.

“Taƙaddamar ta ɗauki ’yan mintoci ne kawai kafin Aboy ya farwa Ayomide  sannan ya daɓa masa wuƙa. Ya mutu kafin mutanen unguwa su kai shi asibiti,” in ji Moyo.

Wani mazaunin yankin mai suna Daniel, ya zargi ofishin ’yan sanda na Onipanu da tsare mutanen da suka je kai rahoton lamarin maimakon su bi sawun wanda ake zargin. “An san shi (wanda ake zargin) da kai wa mutane hari da kwalba, musamman idan aka samu saɓani. Ina jin yana yin hakan ne saboda mahaifiyarsa tsohuwar jami’ar sanda ce.

“ ’Yan sandan Onipanu ma sun tsare mutanen da suka je kai rahoton faruwar lamarin. Maimakon su ƙaddamar da bincike don kamo wanda ake zargin kafin ya tsere daga garin, sai suka mayar da hankali kan shugabannin unguwa da suka kai rahoton lamarin. Sai washegari aka ba su belin kansu,” in ji Daniel.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai