• Home  
  • NEMA ta buƙaci jihohi su ɗauki matakan kariya daga ambaliya
- Babban Labari

NEMA ta buƙaci jihohi su ɗauki matakan kariya daga ambaliya

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta yi kira ga gwamnonin jihohi da u fara ɗaukan matakan riigakafi da nufin kaucewa matsalar ambaliya sakamakon hasashen da aka yi cewa fiye da jihohi 30 na iya fuskantar gagarumar matsalar ambaliya a daminar bana. A cewar saƙon da NEMA ta wallafa a shafinta na X, Shugabar […]

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta yi kira ga gwamnonin jihohi da u fara ɗaukan matakan riigakafi da nufin kaucewa matsalar ambaliya sakamakon hasashen da aka yi cewa fiye da jihohi 30 na iya fuskantar gagarumar matsalar ambaliya a daminar bana.

A cewar saƙon da NEMA ta wallafa a shafinta na X, Shugabar hukumar Zubaida Umar ta yi kira ga jihohin da su gaggauta ɗaukan mataki domin rage tasirin ambaliyar da aka yi hasashen za a samu a wasu yankunan ƙasar.

Sanarwar ta ce wasu daga cikin matakan da ake tsammanin jihohin su ɗauka sun haɗa da sake farfaɗo da shirin tsaftar muhalli duk wata da yawan gyara magudanan ruwa da hanyoyin wucewar ruwa.

Shugabar NEMA ta kuma ce yi kira ga sarakunan gargajiya da malaman addini da ƙungiyoyin matasa da kafafen yaɗa labarai da kamfanoni masu zaman kansu da su tallafa wa ƙoƙarin hukumar wajen kare afkuwar ambaliya a ƙasar

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000