• Home  
  • Tinubu ya koma gida bayan shafe makonni yana hutu a Faransa
- Babban Labari

Tinubu ya koma gida bayan shafe makonni yana hutu a Faransa

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya koma gida, inda ya sauka a birnin Legas, bayan kammala hutun aiki da ya yi a Faransa. Shugaban ya sauka a sashen saukar jiragen shugaban ƙasa na filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja a ranar Talata, inda Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, da wasu manyan jami’ai suka […]

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya koma gida, inda ya sauka a birnin Legas, bayan kammala hutun aiki da ya yi a Faransa.

Shugaban ya sauka a sashen saukar jiragen shugaban ƙasa na filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja a ranar Talata, inda Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, da wasu manyan jami’ai suka tarbe shi.

Mai taimaka wa shugaban kan kafafen sada zumunta, Olusegun Dada, ya tabbatar da isowar shugaban, inda ya wallafa cewa: “Ya sauka. Barka da dawowa, Mista President!”

Tinubu ya bar Abuja ranar 30 ga Agusta domin hutun aikin, inda ya shafe mako guda a Landan kafin ya wuce Paris.

A cewar mai ba shugaban ƙasar shawara kan yaɗa labarai Bayo Onanuga, Tinubu ya tashi daga Paris zuwa Legas, inda ake sa ran zai gudanar da wasu muhimman taruka da shugabannin siyasa da abokan hulɗarsa.

Fadar shugaban ƙasar ta ce Tinubu zai kuma gudanar da taruka na musamman da shugabannin siyasa da abokan hulɗa na tsawon kwanaki, a shirye-shiryen zaɓen 2027.

Ta ce shugaban ya zaɓi fara sauka a Legas ne domin karrama marigayi Cif MKO Abiola, wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na watan Yunin 1993, kuma yana daga cikin fitattun mutanen da suka taka rawa a gwagwarmayar demokuraɗiyyar Najeriya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai