Hukumar wayar da kan jama’a ta ƙasa NOA tare dahaɗin gwiwar cibiyar horas da ƙwararu dake kula da aiyuka ta ƙasa, sun gudanar da gangamin wayar da kan masu ruwa da tsaki kan samun shaidar sahalewa da kuma ƙwarewa ga masu kula da aiyuka.
Gangamin an gudanar dashi ne, a birnin tarayya Abuja, domin sanar da waɗanda abun ya shafa muhimmancin sanya ƙwararru cikin harkokin gudanar da aiyukan gwamnati da masu zaman kansu.
Hukumar NOA ta ilimintar da mazauna birnin matakan yin rijista ga duk masu sha’awa ta hanyoyin da yakamata su bi, don samun shaidar hukumar.
Shugaban cibiyar horas da ƙwararrun, Chief Olabode Afolayen, ya bayyana cewa gangamin yana nufin sanar da jama’a muhimmanci tilasta masu kula da aiyuka da yin rijista da hukumar, inda ya tabbatar da cewa waɗanda suka ƙware ne kawai za a bawa shaidar aiyuka don tabbatar da sahihanci da kuma aiki mai inganci.
Anasa jawabin babban magatakardar hukumar, Henry Ifeanyi Mbadiwe, ya ce ya zama wajibi ga dukan wani mai kula da aikace-aikace ko kuma koyarwa yayi rijista da hukumar , inda yayi gargadin cewa ga duk wanda aka kama ba tare shaidar izinin hukumar ba, zai fuskanci zaman gidan yari na shekaru biyu.
An fara gangamin ne daga tsohuwar sakateriya ta Abuja da Area 3 da 7 da 8 da 10 da kuma 11
