Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana gamsuwarsa kan yadda ya ce gwamnonin ƙasar sun shirya tare da gudanar da zaɓukan fitar da gwani a faɗin jihohisu.
Yayin da yake jawabi a mazaɓarsa ta Ikoyi bayan ya halarci zaɓen, Shugaba Tinubu ya ce ya ji daɗin yadda zaɓen ke tafiya cikin lumana kamar yadda aka tsara.
”Wannan shi ne siyasa, siyasa ta tun daga tushe, inda kowane mambar jam’iyyarmu ke da damar shiga zaɓen kamar ni ma yadda na zo na yi”, in ji shi.
Shugaban Tinubu ya ƙara da cewa hakan ya nuna cewa Najeriya tana da tsarin dimokraɗiyya mai ƙarfi.
”Haƙiƙa na gamsu da yadda gwamnoni suka yi ƙoƙari a jihohinsu, wajen tarukan jam’iyyarmu tun daga matakin mazaɓa da ƙananan hukumomi da kuma zaɓukan fitar da gwani da tantance ƴantakara”, in ji shi.
