• Home  
  • Ebola: An dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a Congo
- Babban Labari

Ebola: An dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a Congo

Hukumomi a Jamhuriyar Dimokraiyyar Kongo sun dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa yankin Bunia babban binin Ituri har illa masha Allahu, saboda barazanar yaduwar cutar Ebola. Sanarwa daga ma’aikatar sufurin ƙasar ta nuna cewa za a tantance jiragen kayan jin ƙai, da na ma’aikatan lafiya, kuma za a bukaci izini daga hukumomin lafiya da na […]

Hukumomi a Jamhuriyar Dimokraiyyar Kongo sun dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa yankin Bunia babban binin Ituri har illa masha Allahu, saboda barazanar yaduwar cutar Ebola.

Sanarwa daga ma’aikatar sufurin ƙasar ta nuna cewa za a tantance jiragen kayan jin ƙai, da na ma’aikatan lafiya, kuma za a bukaci izini daga hukumomin lafiya da na jiragen sama.

Sanarwar ta kara da cewa, ”Wannan matakin na da manufar hana duk wata yaɗuwar cuta da kuma tabbatar da lafiya da amincin fasinjoji, ma’aikatan jirgin, da ma’aikatan filin jirgin.”

Gwamnati ta shawarci ma’aikatan jirgin da su ɗauki matakan kariya da hukumomin lafiya suka bayar. Bunia na ɗaya daga cikin wuraren da cutar Ebola ta ɓarke.

Gwamnatin ba cika dakatar da zirga-zirgar jiragen sama saboda ɓarkewar Ebola ba, inda a yawancin lokuta sai da kamfanonin jiragen saman su yanke shawarar da kansu idan aka samu irin haka.

Sama da mutane 170 da ake zargin sun mutu tun bayan da Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana ɓarkewar cutar.

Ita ma maƙwabciyar ƙasar Uganda a yau asabar, ta sanar da samun rahotannin wasu mutum uku, da suka kamu da cutar, inda yanzu adadin ya kai biyar.ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar zuwa biyar

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000