• Home  
  • Ana ci gaba da ƙidaya ƙuri’a bayan kammala zaɓen gwamnan jihar Ekiti
- Babban Labari

Ana ci gaba da ƙidaya ƙuri’a bayan kammala zaɓen gwamnan jihar Ekiti

Ana ci gaba da ƙidaya ƙuri’a bayan kammala zaɓen gwamnan jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya. Rahotonni sun ce al’ummar jihar da dama ne suka fita domin kaɗa ƙuri’unsu a zaɓen na yau da aka gudanar a faɗin ƙananan hukomomin jihar 16. Bayanai sun ce tun da misalin ƙarfe 7 na safe masu […]

Ana ci gaba da ƙidaya ƙuri’a bayan kammala zaɓen gwamnan jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Rahotonni sun ce al’ummar jihar da dama ne suka fita domin kaɗa ƙuri’unsu a zaɓen na yau da aka gudanar a faɗin ƙananan hukomomin jihar 16.

Bayanai sun ce tun da misalin ƙarfe 7 na safe masu kaɗa ƙuri’a suka fita rumfunan zaɓe, kodayake ba a fara zaɓen ba sai da ƙarfe 8:30 a wurare da dama.

An jibge tarin jami’an tsaro a rumfunan zaɓe da wuraren tattara sakamakon zaɓen domin bayar da tsaro a lokacin zaɓukan da kuma ƙidaya ƙuri’u.

Ƴantakara fiye da 10 ne suka fafata a zaɓen, ciki har da gwamnan jihar mai ci na jam’iyyar APC da ke neman wa’adin mulki na biyu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000