• Home  
  • Majalisar Wakilai ta janye kudirinta kan ‘yan sandan jihohi tare da yin nazari kan buƙatar Tinubu
- Babban Labari

Majalisar Wakilai ta janye kudirinta kan ‘yan sandan jihohi tare da yin nazari kan buƙatar Tinubu

Majalisar Wakilai ta janye kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ta gabatar domin kafa rundunar ‘yan sandan jihohi, inda ta yanke shawarar mayar da hankali kan irin wannan kudiri da bangaren zartarwa karkashin Shugaba Bola Tinubu daya aike mata. An bayyana hakan ne a zaman majalisar na ranar Talata, inda aka karanta kudirin da bangaren […]

Majalisar Wakilai ta janye kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ta gabatar domin kafa rundunar ‘yan sandan jihohi, inda ta yanke shawarar mayar da hankali kan irin wannan kudiri da bangaren zartarwa karkashin Shugaba Bola Tinubu daya aike mata.
An bayyana hakan ne a zaman majalisar na ranar Talata, inda aka karanta kudirin da bangaren zartarwa ya gabatar karo na farko da na biyu.
Daga nan ne aka mika kudirin ga Kwamitin Majalisar kan Gyaran Kundin Tsarin Mulki domin ci gaba da nazari da duba cikakkun tanade-tanadensa.
Matakin na nufin dakatar da ci gaba da aikin kudirin da Majalisar ta gabatar a baya, yayin da za ta mayar da hankali wajen nazarin kudirin da gwamnatin tarayya ta gabatar.
Ana sa ran kwamitin zai yi cikakken nazari kan muhimman tanade-tanaden kudirin kafin ya dawo gaban zauren majalisar domin ci gaba da matakan amincewa da sh

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000