• Home  
  • Tsohon shugaban FRSC, Dauda Ali Biu, ya rasu yana da shekara 62
- Labarai

Tsohon shugaban FRSC, Dauda Ali Biu, ya rasu yana da shekara 62

Tsohon shugaban Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), Dauda Ali Biu, ya rasu yana da shekara 62 a duniya. Marigayin ya rasu ne da yammacin ranar Lahadi a wani asibiti da ke Abuja, bayan fama da rashin lafiya. Ɗan uwan marigayin, Adamu Isa Gunda ne, ya tabbatar da rasuwar, inda ya ce za a dawo […]

Tsohon shugaban Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), Dauda Ali Biu, ya rasu yana da shekara 62 a duniya.

Marigayin ya rasu ne da yammacin ranar Lahadi a wani asibiti da ke Abuja, bayan fama da rashin lafiya.

Ɗan uwan marigayin, Adamu Isa Gunda ne, ya tabbatar da rasuwar, inda ya ce za a dawo da gawarsa daga Abuja zuwa unguwar Chikaji da ke Sabon Gari, Zariya, domin yi masa jana’iza.

Biu, wanda aka haifa a shekarar 1964 a Ƙaramar Hukumar Sabon Gari da ke Jihar Kaduna, yana riƙe da sarautar gargajiya ta Jagaban Sabon Gari.

Ya rasu ya bar mata ɗaya da ’ya’ya biyar.

Marigayin ya jagoranci hukumar FRSC daga watan Yulin 2022 zuwa shekarar 2024, bayan ya shafe shekaru da dama yana aiki a hukumar tare da riƙe muƙamai daban-daban.

Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne, ya naɗa shi muƙaddashin shugaban hukumar a watan Yulin 2022, bayan ritayar Boboye Oyeyemi, wanda ya gabace shi.

Kafin naɗin nasa, Biu ya kasance mataimakin shugaban hukumar mai kula da harkokin kuɗi a hedikwatar FRSC da ke Abuja.

Ya shiga aikin hukumar a shekarar 1988, inda ya samu ɗaukaka a matakai daban-daban.

A shekarar 2014, ya zama mataimakin kwamandan hukumar mai kula da harkokin kuɗi da lissafi, kafin daga bisani a ɗaga shi zuwa matsayin mataimakin shugaban hukumar a shekarar 2016.

Marigayin ya yi digiri na biyu a fannin Gudanar da Kasuwanci (MBA) a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

An yi jana’izar marigayin a ranar Litinin a gidansu da ke unguwar Chikaji, Sabon Gari, Zariya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai