• Home  
  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da ke ketare su zuba jari a Nijeriya
- Kasuwanci

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da ke ketare su zuba jari a Nijeriya

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Nijeriya ya yi kira ga ‘yan ƙasar da ke ƙetare su wuce matakin tura kuɗi gida kawai su fara gina wasu kaso masu samar da abubuwa a cikin tattalin arzikin ƙasar. Tinubu ya yi wannan kiran ne yayin da ake buɗe wani taron tattalin arziki na ‘yan Nijeriya da ke […]

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Nijeriya ya yi kira ga ‘yan ƙasar da ke ƙetare su wuce matakin tura kuɗi gida kawai su fara gina wasu kaso masu samar da abubuwa a cikin tattalin arzikin ƙasar.

Tinubu ya yi wannan kiran ne yayin da ake buɗe wani taron tattalin arziki na ‘yan Nijeriya da ke ƙetare (NIDEC) na shekarar 2026, da ake yi a cibiyar taro ta Apollo da ke, Toronto, a ƙasar Kanada.

Shugaban da ya samu wakilcin Shugaban Ma’aikatansa, Femi Gbajabiamila, ya bayyana ‘yan Nijeriya da ke ƙetare a matsayin hujja a aikace cewa ‘yan Nijeriya za su iya gogayya da waɗanda suka fi ƙwarewa a duniya.

“Nijeriya na ganinku. Nijeriya na ganinku da daraja. Nijeriya na buƙatarku,” kamar yadda daraktan watsa labarai da hulɗa da jama’a na hukumar NiDCOM da ke kula da ‘yan Nijeriya da ke ƙetare, Abdur-Rahman Balogun, ya ambato shugaban ƙasar yana cewa.

Ya bayyana cewa yayin da girman tattalin arziki da kuma ɗorewar tsarin siyasa ƙasa ke nuna inda mutane ke saka kuɗaɗenku, manuniya a Nijeriya na nuna ƙasar a matsayin wadda ke kan farfaɗowa na gaske.

Shugaban ƙasar ya yi ishara ga haɓakar kimar tattalin arziki a ma’aunin GDP da kashi 3.89 cikin 100 a cikin rubu’i na farko na shekarar 2026, inda fannin ƙere-ƙere ya haɓaka da kashi 3.29 cikin 100, kuma hawhawar farahi ya ragu da kashi 15.91 cikin 100, kuma ajiyar kuɗin ƙetaren ƙasar ta ƙarƙre shekarar 2025 a dala biliyan $45.4.

Tinubu ya jaddada cewa Asusun Bada Lamuni IMF ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai ƙaru da kashi 4.1 cikin 100 a shekarar 2026 kuma ya ce gyaran da ya yi wa tattalin arzikin ƙasar cikin shekaru uku da suka gabata ta inganta tattatlin arzikin ƙasar da kuma juriyarsa.

Ya bayyana cewa Bankin Duniya ma ya bayyana ci-gaban da ƙasar ta samu wajen dawo da tattalin arziki mai ɗorewa da kuma ƙarfafa ajiyar kuɗaɗen ƙataren ƙasar da tabbatar da ɗorewar ci-gaban ƙasar.

Shugaban ya ce ko da yake tura kuɗi gida Nijeriya na da muhimmanci wajen taimaka wa miliyoyin gidajen ‘yan Nijeriya wajen biyan kuɗin makaranta da magani da ƙananan masana’antu, yanzu ya kamata amfanin kuɗaɗen su zarce wannan .

Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da ke ƙetare su tura jari zuwa fannin sarrafa amfanin gona da kiwon lafiya da fasaha da makamashi da gidaje da jigilar kayayyaki da haƙar ma’adinai da ilimi da ƙera abubuwan fitarwa ƙetare.

Shugaban Tinubu ya yi kira ga ‘yan ƙasar da ke ƙetare su haɗa kai wajen zuba jari maimakon rarraba jarinsu kuma su tabbatar da cewa an bi da jarinsu yadda ya dace bisa jagorancin ƙwararru.

Ya ce dole gwamnati ta samar musu wani yanayi na dokoki da za a iya hasashen tafiyarsa da bayyana gaskiya game da yadda aikin gwamnati ke tafiya da hidindimu na ofisoshin jakadanci da kuma kare su daga damfara

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000