• Home  
  • Ana zargin wata mata da kashe mijinta saboda ya na shirin ƙara aure a Kano
- Babu Rukuni

Ana zargin wata mata da kashe mijinta saboda ya na shirin ƙara aure a Kano

Wata mata mai suna Bilkisu Sani, mazauniyar ƙaramar hukumar Rogo a Jihar Kano, ta shiga hannun ’yansanda bisa zargin kashe mijinta, Hafizu Gausu, wanda ake zargin yana shirin ƙara aure. Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:00 na yammacin Juma’a a yankin Katsalle da ke garin Rogo. Wani […]

Wata mata mai suna Bilkisu Sani, mazauniyar ƙaramar hukumar Rogo a Jihar Kano, ta shiga hannun ’yansanda bisa zargin kashe mijinta, Hafizu Gausu, wanda ake zargin yana shirin ƙara aure.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:00 na yammacin Juma’a a yankin Katsalle da ke garin Rogo.
Wani mazaunin yankin, Auwal Kazagi Rogo, ya shaida wa Daily Trust cewa jama’a sun garzaya wurin bayan sun ji ihun matar marigayin tana cewa an yanka mijinta.
Sai dai Kazagi ya ce bayan isar jama’a wurin, an gano cewa ba yanka aka yi wa Gausu ba, illa dai an buge shi a kan sa da wani abu mai nauyi, lamarin da ya sa ya faɗi cikin jini kuma ya mutu.
Ya kuma ce an ga alamar cizo a kunnen marigayin.
Bayan faruwar lamarin ne aka kira ’yan sanda, waɗanda suka kwashe gawar domin gudanar da bincike.
A cewar Kazagi, ana zargin Gausu ya na da niyyar auren wata mata a matsayin matarsa ta biyu, abin da ya jawo yawan saɓani tsakaninsa da Bilkisu.
An ce dattawa sun taɓa shiga tsakani domin sasanta rikicin, amma rashin jituwa ta ci gaba.
Kazagi ya ce ’yan sanda sun kama Bilkisu a matsayin wadda ake zargi da hannu a mutuwar mijinta, yayin da bincike ke ci gaba.
An binne Gausu a safiyar Asabar a Rogo bisa tsarin addinin Musulunci.
Marigayin da Bilkisu sun shafe kusan shekaru bakwai da aure, kuma suna da ’ya’ya biyu. Rahotanni sun ce Bilkisu na da ciki a lokacin rasuwar mijin nata.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai