Rundunar yan sandan jihar Kano ta rabawa iyalan jami’an ’yan sanda 62 tallafin da ya kai Naira miliyan 34 da dubu 309 da 73 da kobo 70.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya gabatar da cak din ga wadanda suka amfana a hedikwatar rundunar da ke Bompai, Kano.
Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce tallafin na karkashin tsarin inshorar rayuwa da hatsari na jami’an ’yan sanda, wanda babban sufeton yan sandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, ya samar domin tallafa wa iyalan jami’an da suka mutu wajen aiki da kuma jami’an da suka samu raunuka.
CP Bakori ya ce ko da yake babu wani kudi da zai maye gurbin rayuwar jami’in da ya rasu, tallafin wata hanya ce ta tausayawa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a bakin aiki.
Ya bukaci wadanda suka amfana da su yi amfani da kudaden wajen kula da iyalansu, musamman ilimin ’ya’yansu.
A nata bangaren, daya daga cikin wadanda suka amfana, Malama Safiya Abdullahi Adamu, ta gode wa rundunar bisa tallafin, tare da yin addu’ar Allah ya ji Kan jami’an da suka rasu.
