Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa bai halarci babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) ba karo na uku a jere.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Lahadi, Atiku ya ce rashin halartar taron sau uku a jere abu ne da ya saɓa ƙa’ida, wanda hakan na iya yin tasiri ga hulɗar Najeriya da ƙasashen duniya..
Ya ce akwai buƙatar fadar shugaban ƙasa ta fayyace ko akwai wani abin da ke hana Tinubu zuwa Amurka, domin “ƴan Najeriya na da haƙƙin sanin dalilin rashin halartar taron sau uku a jere”.
Ya bayyana cewa taron UNGA na ɗaya daga cikin muhimman wuraren da shugabannin ƙasashe ke tattauna batutuwan tsaro, kasuwanci da ci gaba tare da neman jari da haɗin gwiwa da sauran ƙasashe.
A cewarsa, duk da cewa Shettima na iya wakiltar Najeriya, amma bai kamata hakan ya maye gurbin kasancewar shugaban ƙasa da kansa ba.
Atiku ya kuma yi zargin cewa wataƙila ko tsohuwar shari’ar “ƙwace kadarori” da gwamnatin Amurka ta taɓa gudanarwa kan wasu kuɗaɗe da ake dangantawa da Tinubu a shekarun 1990, “dalilin da ke sanya shugaban ƙasar gujewa halartar tarukan a ƙasar Amurka”.
Ya kuma ɗiga ayar tambaya kan rahotannin da ke cewa an tanadar wa Tinubu kujera kusa da Shugaban Amurka Donald Trump a taron, amma daga ƙarshe ya ƙi halarta.
Tinubu bai halarci zaman Majalisar Ɗinkin Duniya na shekarun 2024, 2025 da 2026 ba, inda a kowanne lokaci yake tura Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilce shi.
