• Home  
  • APC ta ƙalubalanci Atiku ya yi bayani dalla-dalla kan yadda zai dawo da tallafin mai
- Babban Labari

APC ta ƙalubalanci Atiku ya yi bayani dalla-dalla kan yadda zai dawo da tallafin mai

Jam’iyyar APC ta buƙaci tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi cikakken bayani kan yadda yake shirin aiwatar da abin da ya kira “tallafin samar da man fetur a matatun cikin gida domin rage farashin fetur”. A cikin wata sanarwa da kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, Dele Alake, ya sanya […]

Jam’iyyar APC ta buƙaci tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi cikakken bayani kan yadda yake shirin aiwatar da abin da ya kira “tallafin samar da man fetur a matatun cikin gida domin rage farashin fetur”.

A cikin wata sanarwa da kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, Dele Alake, ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta ce akwai ayar tambaya game da shirin Atiku a tsarin doka da tattalin arziki da ya kamata ya amsa.

APC ta ce ya kamata ɗantakarar jam’iyyar adawa ta ADCn ya bayyana yadda shirin zai yi aiki ƙarƙashin Dokar Man Fetur (PIA), da kuma yadda zai tabbatar da rage farashin fetur ga masu amfani.

Jam’iyyar ta kuma buƙaci ya bayyana kuɗin da za a kashe wajen aiwatar da shirin, daga inda kuɗaɗen za su fito, da hanyoyin da za a bi wajen hana karkatar da tallafin ko safarar mai zuwa ƙasashe maƙwabta.

APC ta ce Atiku ya taɓa sukar tsarin tallafin fetur a baya tare da alƙawarin kawo ƙarshensa, don haka ya kamata ya yi bayanin dalilin da ya sa yanzu yake goyon bayan dawo da wani nau’in tallafi.

Jam’iyyar ta ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta fi mayar da hankali kan samar da hanyoyin sufuri masu amfani da iskar gas da lantarki, maimakon komawa tsarin tallafin fetur.

A cewar APC, har sai Atiku ya gabatar da cikakken bayani dalla-dalla kan yadda shirinsa zai yi aiki da kuma kuɗin da zai laƙume za ta fahimta, domin yanzu alƙawari ne kawai ya yi da bai fayyace yadda za a aiwatar da shi ba

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai