• Home  
  • Yara mata 4 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa
- Labarai

Yara mata 4 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa

Yara mata huɗu sun riga mu gidan gaskiya a Jihar Jigawa, bayan kwale-kwalen ɗaukar fasinjoji ya kife a tsakiyar tafkin Dudduru, yayin da yake kan hanyarsa na zuwa kasuwa. Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4 na yammacin ranar Laraba, 23 ga watan Satumba, 2026, a tafkin da ke kusan kilomita uku daga ƙauyen […]

Yara mata huɗu sun riga mu gidan gaskiya a Jihar Jigawa, bayan kwale-kwalen ɗaukar fasinjoji ya kife a tsakiyar tafkin Dudduru, yayin da yake kan hanyarsa na zuwa kasuwa.

Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4 na yammacin ranar Laraba, 23 ga watan Satumba, 2026, a tafkin da ke kusan kilomita uku daga ƙauyen Kwadige, a Ƙaramar Hukumar Dutse.

Hukumar Sibil Difens (NSCDC) a Jigawa ce, ta tabbatar da faruwar hatsarin.

A cewar sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, ASC Badruddeen Tijjani Mahmud, ya fitar, kwale-kwalen na ɗauke da mutane takwas ne daga Kwadige zuwa kasuwar Chai Chai Sabuwa lokacin da ya kife.

Binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa iska mai ƙarfi da ake yi a lokacin na iya kasancewa ɗaya daga cikin abubuwan da suka haddasa hatsarin.

Daga cikin fasinjojin, an ceto mutum huɗu, yayin da sauran huɗun suka rasu.

Waɗanda suka rasu sun haɗa da Hasiya Mu’azu mai shekaru 13, Hauwa Lawan mai shekaru 13, Fatima Lawan mai shekaru 12 da Dawsiyya Lawan mai shekaru 13.

An yi jana’iza tare da binne gawarwakinsu bisa tsarin addinin Musulunci.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai